Yabon Gwani Ya Zama Dole; Sharhi Akan Gudumuwar Danmajen Gwandu
Injiniya Farouk Ahmed Umar (Danmajen Gwandu/Gamjin Kabi): Jagoran Ƙarfafa Goyon Bayan Manufofin “Renewed Hope” Da Taimakon jama'a a Kebbi da Yankin Arewa maso Yamma
Daga: Aminu Abdullahi Garba
Gamji Dan ƙwarai; yabon gwani ya zama dole!.
A kowanne yanayi na siyasa, mutane kaɗan ne ke sadaukar da komai nasu don ci gaban al’ummarsu.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan jajirtattun shi ne Injiniya Farouk Ahmed Umar, FNSE, FCIA, MCOREN, NPOM (Ɗanmajen Gwandu/Gamjin Kabi).
Tafiyarsa cike take da sadaukarwa, taimakon al'umma, kishin ƙasa, haɗe da gudanar da shugabancin da zai amfanar da al'umma na dindindin.
A nasa ɓangaren, ya zama ginshiƙi mai ƙarfi wajen tabbatuwar manufofin mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da ƙarfafa jagorancin Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) da kuma tabbatar da ƙarfin jam’iyyar 'All Progressives Congress' (APC) a faɗin Jihar Kebbi da yankin Arewa maso Yamma.
Ɗanmajen Gwandu ya kasance jigo ne a fagen haɗa kan jama’a domin ci gaba da nasarar jam'iyar APC. Duk da ƙarancin abin da yake da shi, yana ci gaba da bayarwa ba don yana neman wata kujera ta siyasa ba, sai don ya yi imani da manufar taimakon jama'a. Ko da yake yana riƙe da muƙamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da sararin Samaniyar Nijeriya watau 'Nigerian Airspace Management Agency (NAMA),' hakan bai hana shi kasancewa kusa da jama’arsa ba.
Jumma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Wannan ne ya sa a fagen siyasar Jihar Kebbi, ana fara jin kiraye-kiraye daga sassa daban-daban—na roƙon Mai Girma Dr Nasir Idris Kauran Gwandu da ya duba waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen kare jam’iyya da manufofinta. Waɗanda suka kasance masu biyayya, suka tallata kuma suka ɗaukaka martabar APC a kowane mataki, tare da nuna cikakken goyon baya ga jagorancinsa. Mutane da dama na ganin lokaci ne da ya dace a gane irin waɗannan mutane tare da ba su damar tsayawa takara domin su ƙara bayar da gudunmawa.
Ɗanmajen Gwandu na daga cikin irin waɗannan jajirtattun mutane. Jagora ne a fagen tallata manufofin “Renewed Hope”, kuma duk lokacin da ya samu dama, yana dawowa gida Kebbi domin taimaka wa jama’arsa. Daga ƙaramar hukuma zuwa wata—a dukkan ƙananan hukumomi 21 dake jahar Kebbi—yana zagayawa a matsayin ɗan gida domin taimakawa jama'a. Yana sauraro, yana tallafawa, yana bayarwa. Sau da yawa ma yana bayarwa ba tare da ya ma san ya bayar ba. Tasirinsa yana bayyana a cikin al’umma, a cikin ayyukan da yake yi a ɓoye, da kuma rayukan da yake taɓawa ba tare da hayaniya ba. Hakan ya sa ya zama mikiya mai hangen nesa, wanda yake hango matsalolin al'umma da yadda za a magance su tun da wuri.
Abin da ya bambanta shi ba matsayinsa kawai ba ne, sai zuciyarsa. A cikin yanayin da mutane da yawa ke rike da manyan mukamai, tawali'unsa da kusancinsa da jama’a ne suka sa ya zama na musamman—abin koyi ga kowa. Yana zama tsani tsakanin shugabanci da talakawa, yana nuna ainihin ma’anar hidima.
Kasancewarsa murucin kan dutse, bai fito ba sai da ya shirya, ya sa mutanen Kebbi ke dakyakkyawar fata a zuƙatansu—don ganin jajircewarsa da hangen nesansa, haɗe da ƙwarewarsa a shugabanci ba za su tafi a banza ba. Mutane da dama na ganin cewa ba shi damar tsayawa takara a 2027 ko 2031 idan Allah Ya kaimu, zai buɗe ƙofa domin ya ƙara taimakawa walwalar jama’a da ci gaban al’umma da yake wakilta.
Fata nagari lamiri, saboda haka, fata na nan daram—cewa Dr Nasir Idris Ƙauran Gwandu zai duba zurfin sadaukarwarsa, ya kuma ba Ɗanmajen Gwandu dama ya taka rawar da ta dace. Damar ci gaba da hidima, da ƙara bayarwa, da kuma daidaita ƙoƙarinsa da wata babbar hanya—wadda za ta nuna manufar ɗaga rayuwar jama’a da ci gaba da cika alkawarin “Renewed Hope”.
Nagari Nakowa- inji malam Bahaushe; tabbas Danmajen Gwandu nagari ne, abin kauna ga kowa.

Post a Comment
0 Comments