Tarihin Dan'majen Gwandu (Kashi Na 12)

ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

           ( Kashi Na 12)


 RA'AYIN MAGABATA AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da  kuma wajen zaben shugabanni.


A wannan kashi na 12, kuma na karshe a wannan sharhi akan takaitaccen  tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamu kawo ra'ayin MAGABATA watau manyan mutane akan rayuwar Dan'majen Gwandu 



1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 12:

Magabata da suka hada da shugabanin kasa, sarakuna da sauran su, sun jinjina wa Dan'majen Gwandu bisa sanin aiki, ilimi da dattako.

Ba tare da bata lokaci ba, ga kadan daga hukuncin magabata akan rayuwar Dan'majen Gwandu:

1- SHUGABA BOLA AHMED TINUBU 
 _..Na amince da nada Injiniya Ahmed Umar Farouk a matsayin shugaban hukumar kula da sararin samaniya ta Nigeria (MD Nigerian Airspace Management Agency NAMA) bisa gamsuwa da kwarewan sa da ilimin sa a fannin lamuran jiragen sama, Ina da da kyakyawan fatar zai kawo canji Mai ma'ana a fannin jiragen sama a Nijeriya_ ..
_______________________________________

2-SHUGABA MUHAMMADU BUHARI
..Gwamnatin tarayya Nijeriya karkashin jagoranci na ta gamsu da himma da kwazo da sanin aiki da Kuma kishin kasa da Injiniya Ahmed Umar Farouk ya nuna akan ayukkan sa, bisa haka muka yanke shawaran girmama shi da lambar yabo ta kasa(National Productivity Order of Merit Award-NPOM)..
_____________________________________

3- GWAMNAN JIHAR KEBBI DR. NASIR IDRIS
..M.D Injiniya Ahmed Umar Farouk (Dan'majen Gwandu) haziki ne kuma amintacce magoyi bayan Gwamnatin APC ne a matakin tarayya da kuma matakin jaha; mun yaba Kuma muna goyon bayan kungiyar TKG da ya kirkiro.....
_____________________________________


4- SARKIN GWANDU; GEN.  MUHAMMAD ILIYASU BASHAR
..Masarautar Gwandu ta amince da nada Injiniya Ahmed Umar Farouk a matsayin DAN'MAJEN GWANDU bisa gamsuwa da nasaba, ilimi, hazaka da kyakyawan ma'amala sa da mutane...
___________________________________

5- SARKIN KABIN ARGUNGU; ALH. SAMA'ILA MUHAMMAD MERA, CON
..Injiniya Ahmed Umar Farouk mutum ne mai kishin kasa da sanin ya kamata, la'akari da wayanan kyawawan halayan sa suka sa wannan masarautar Argungu (Argungu Emirate) ta bashi sarautar GAMJIN KABI....
____________________________________

2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? 

 Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu


3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?

 Bautan Allah, Alheri, Kyauta,  da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments