Tarihin Dan'majen Gwandu (Kashi na 10)
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 10)
SHAHARAN DAN'MAJEN GWANDU A FANNIN JIRAGEN SAMA
Daga Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
A wannan kashi na 10, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan shaharan sa akan harkokin jiragen sama.
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 10:
Idan za a tuna, a kashi na biyar (5) na wannan sharhi munyi bayani akan ilimin da Allah Ya albarkaci Dan'majen Gwandu da shi da suka hada da digiri a fannin Injiniya da babban digiri (watau masters degree) har guda biyu da sauran su.
A wannan karon zamuyi bayani ne akan shaharan da Allah Yayi masa a fannin ilmin jiragen sama.
DAN'MAJEN Gwandu ya sami wannan shahara ce ta hanyar halarta kwasa-kwasai (courses) da dama a fannin lamuran jiragen sama
TUN FARKO..:
Tun farko Injiniya Ahmed Umar Farouk (Dan'majen Gwandu) ya taba zama zakara a matsayin Injiniya mafi kwazo a makarantar koyon tukin jiragen sama da ke Zaria a shekara ta 2004. watau 'OVERALL BEST STUDENT of Air Traffic Safety Engineer Personnel'; Nigerian College of Aviation and Technology (NCAT), Zaria, 2004.
Baya ga haka; Dan'majen Gwandu ya taba lashe lambar yabo da hukumar kula da filayen jiragen sama (NAMA) ke bayar wa, sau biyu a jere ga juna; a matsayin manaja Mai kula da filayen jiragen sama mafi sanin aiki a Nijeriya, a shekara ta 2007 da Kuma shekara ta 2008 ( watau Two times Award winner of best Airspace Manager by Nigerian Airspace Management Agency (NAMA), 2007 and 2008.
Bayan wannan, Dan'majen Gwandu ya kara samun damar kwarewa da shahara a duniyar jiragen sama ta hanyar halarta kwasa-kwasai kamar haka:
- Dan'majen Gwandu ya halarci Kwas na musanman da ake kira ' ATSEP Licensing Course No.3 (NCAT.ZARIA)
- Dan'majen Gwandu ya halarci Kwas na musanman da ake kira 'Electrical Machine/Generator maintenance
- Dan'majen Gwandu ya halarci Kwas na musanman da ake kira ICAO CNS/ATM Workshop
- Dan'majen Gwandu ya halarci Kwas na musanman da ake kira 'Aviation management ' da sauran su, da sauran su.
Wayanan kwasa-kwasai sun taimakawa Injiniya Ahmed Umar Farouk kwarewa da shahara akan fannin jiragen sama, har zuwa yau da Allah ya bashi ikon zama shugaban hukumar kula da sararin samaniya ta Nigeria; watau MD, Nigerian Airspace Management Agency (NAMA)
Allah Ya taya riko; Ya kara basira da hazaka; Amin Ya hayyu, Ya Qayyum👏🏻
Mu hadu a kashi na 11:
A kashi na gaba watau Kashi na 11, zamuyi karin bayani akan ayukkan alherin Dan'majen Gwandu In Sha Allah.
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments