Tarihin Dan'Majen Gwandu (Kashi Na 6)
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 6)
Aikace-aikacen Dan'Majen Gwandu
Daga Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
A wannan kashi na 6, akan takaitaccen tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan Ma'aikatun da ya yi aiki.
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 6:
Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan'Majen Gwandu) ya yi aiki a ma'aikatu biyu kafin ya fara aiki da hukumar Kula da sararin samaniya ta Nigeria Watau Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA':
Da farko Injiniya Ahmad Umar Farouk ya fara aiki a kamfanin buga siminti dake Jahar Sokoto (watau Sokoto Cement Company of Northern Nigeria) tsakanin shekara ta 1985 zuwa 1986, daga nan sai ya koma makaranta yayi Digiri, bayan kammala karatun Jami'a da kuma bautar kasa (NYSC) a shekara ta 1989, sai ya samu aiki a Ma'aikatar kwadago ta Gwamnatin Tarayya (Watau Federal Ministry of Labour and productivity) inda yayi aiki a Jahar Lagos da kuma babban birnin tarayya Abuja.Ya rike mukamai da dama, cikin su har da Shugaban sashe na Ma'aikatar (Watau Head of the station) da Kuma babban jami'i mai tantancewa Watau 'Chief Trade Testing Officer (CTTO)' duk a Ma'aikatar kwadago ta Gwamnatin Tarayya.
Injiniya Ahmad Umar Farouk ya canza aiki daga Ma'aikatar kwadago zuwa hukumar kula da sararin samaniya ta Nigeria (Watau Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') a shekara ta 2002.
Mu hadu a kashi na 7 domin samun cikakken bayani akan matsayin da Dan'Majen Gwandu ya rika har zuwa kololuwan mukamin da yake a yanzu Watau 'Managing Director (MD); Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA').
( A kashi na gaba Watau Kashi na 7, zamuyi bayani akan aikace aikacen Dan'Majen Gwandu a hukumar 'Nigeria Airspace Management Agency' (NAMA) har zuwa wannan matsayin na 'MD' In Sha Allah)
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
Publisher Kebbi-Trust Online Newspaper
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments