Kebbi-Trust Online Newspaper
Asan Mutum; Asan Halinsa; Asan Aikin Sa: SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 1)
Daga: Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da ya kamata mutane suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
Babban kuskure ne yin ma'amala ko zaben mutumin da ba a san shi ba; ba a san halin sa ba, ba a kuma san aikin sa.
Hausawa na cewa ajiya maganin wata rana; bisa wannan ne nike son bayyana wane ne Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') domin ilmantar da al'ummar Jahar Kebbi tarihin wannan dan-baiwa da Allah Ya ba Jahar Kebbi kyauta.
1- Asan Mutum: WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Ataikaice Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu) jika ne ga Sheikh Abdullahi Ibn Fodiyo; wanda ya assasa masarautar Gwandu, Kuma Sarkin Gwandu na farko. Ma'ana Dan'Majen Gwandu cikakken jinin sarautar Gwandu ne gaba da baya.
( A kashi na gaba zamuyi bayani akan nasabar sa a gidan Abdullahin Gwandu, ilimin sa, aikace aikacen sa har zuwa wannan matsayin nasa na MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA' In Sha Allah)
2- Asan Halin sa: MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya da rikon amana sune gimshikan halayar Dan'Majen Gwandu; idan kana son kaga fushin Injiniya Ahmad Umar Farouk to shirya rashin gaskiya ka gayyace shi, komai girman ka zai nisanta kanshi da kai; Misali, a yan' kwanakin nan anga wasu mutane na kusa da Gwamna sun kirkiro da wata kungiya mai rikitaccen suna, da Dan'Majen Gwandu yaga rashin gaskiya a wannan kungiyar, duk kusanci sa da Gwamna kaitsaye ya fito ya nisanta kan sa da su.
(A kashi na gaba zamuci gaba da kawo bayanai da misalai akan halayan Dan'Majen Gwandu In Sha Allah)
3- Asan Aikin Sa: MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)
Alheri, kyauta da tausayin bayin Allah na daya daga cikin ayukkan Dan Majen Gwandu.
Yadda Allah Ya sanyawa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) shawan yin alheri da kyauta mai yawa: haka Dan-sa Injiniya Ahmad Umar Farouk ya ke. Abin sa abin jama'a ne. Ba wanda zaiyi ma'amala da Dan'Majen Gwandu ya renashi sai dai ya yabe shi.
( A kashi na gaba zamuci gaba da kawo bayanai da misalai akan Ayukkan ahairan Dan'Majen Gwandu In Sha Allah)
_____________________
Post a Comment
0 Comments