Kebbi-Trust Online Newspaper

DA DUMI-DUMI: *Uwar Jam'iyar APC Ta Jihar Kebbi Ta Soke Kungiyar 9/11*

A matakin rigakafi don dinke matsalolin da ke neman kunno kai a Jam'iyar APC a jihar Kebbi, uwar Jam'iyar APC a matakin jaha ta rusa Sabuwar kungiyar 9/11

Sanarwa ta fito ne daga bakin Sakataren yada labarai na Jam'iyar APC, Alhaji Isah Assalafi a cikin shiri na musanman da gidan Radiyon Rayhaan yayi da shi a daren jiya talata 25/2/2025.

Assalafi yace tun farko ma Jam'iyar APC bata San da wannan kungiyar 9/11 ba, asalima cikin kuskure ne Wani babban mutum ya furta wannan sunan a wajen wani taro.

Tun farko an zargi 9/11 da yunkurin yiwa Gwamna zagon kasa, zargin da magoya bayan su Suka Karya ta.

Kakakin Jam'iyar APC ya yabawa Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) da Shugaban kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu bisa ayukkan ci gaban kasa da suke aiwatarwa a Jihar Kebbi.

 Da karshe yayi kira ga Ya'yan Jam'iya da su ci gaba da baiwa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu da Shugaban kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu hadin kai da goyon baya domin su ci gaba da ayukkan alherin da suka fara.

Post a Comment

0 Comments