Kebbi-Trust Online Newspaper
Sabuwar Karamar Hukumar Dandi:
Ayukkan Ci Gaban Kasa Da Al'umma Da Dr. Mansur Ya Tsara Yi A Mazabar Fana
Dan takaran kujeran Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Dandi a karkashin jam'iyar APC Dr. Mansur Isah Kamba ya kuduri aiwatar da ayukkan ci gaban kasa da dama a Mazabar Fana (Fana Ward) Idan aka zabeshi a matsayin Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Dandi a 31/8/2024.
Wayannan ayukkan dai mutanen Fana da kansu ne suka zakulo su a lokacin da Dr. Mansur ya yayi ganawa da su a lokacin da yake rike da kujeran kantoman riko.
Ga jerin gwanon ayukkan da In Sha Allah za a aiwatar a Mazabar Fana idan aka zabi Dr. Mansur na jam'iyar APC, Kuma aka sami wadatattun kudin yin ayukkan:
1- Gina hanyar Fana zuwa Banizumbu
2- Gina hanyar Fana zuwa Maigwaza zuwa Dukushi
3-Gina hanyar Fana zuwa Maidaji
4- Samar da wutan lantarki a Tungan Zagi
5- Gina kwalbati a kusa da gidan Dukiya Fana da kusa da gidan Madawaki a Fana
6- Gina kwalbati a hanyar Tungan Baraje zuwa Tungan Sansani
7-Gina dakin Shan magani a Unguwar Bakoshi
8- Gyara asibitin garin Maidaji
9- Gina makarantar firamari a garin Isakaina da Tungan Nori
10- Samar da fitillon kan titi a garin Isakaina da dukkan mazabun dake Fana
11- Gewaye makabartan garin Zagi
12- Gyaran asibitin garin Tungan kaka
13- Samar da famfo Mai aiki da hasken rana a garin Fana
14- Koyawa matasa da mata ayukkan Yi domin dogaro da kai
15- Samar da injimin ban ruwa Mai aiki da hasken rana da takin zamani a dukkan mazabun dake Fana
16- Gyara sakatariyan 'Fana Development Area'
17- Samar da malaman aikin lafiya
18- Gyara GSS Fana
19- Gina makarantar koyon aikin hannu
20- Gyara fadar Sarkin Fana
21- Gyara kwalbati a garin Nibo
22- Samar da Karin malaman makarantar
23- Samar da Karin Jami'an tsaro
24- Samar da kayan aiki a asibitotin Fana
A biyo mu a fitowa na gaba domin jin ayukkan da Dr. Mansur ya tsarayi a sauran mazabun dake Dandi.
______________________
Ahmad Umar
07038182929
Post a Comment
0 Comments