Sabuwar Karamar Hukumar Dandi

Sabuwar Karamar Hukumar Dandi


Dr. Mansur Ya Fara Ceto Fanni Ilmi A Dandi: Ya Dauki Sabbin Malamai Aiki

A kokarin sa na farfado da darajar ilmi a karamar hukumar sa, Shugaban Karamar hukumar Dandi mai jiran rantsarwa, Dr. Mansur Isah Kamba ya dauki sabbin Malamai aikin karantarwa.

Malaman sun hada da masu shaidar ilmin Digiri, HND da Kuma masu NCE.
Bayan haka sai da aka tantance su aka tabbatar da zasu iya aikin karantarwan.

Idan za a tuna, Dr. Mansur ya kafa kwamiti na masana da dattawa domin bashi shawaran yadda za a farfado da kowane fanni rayuwa a Dandi.
A fanni Ilmi an gano akwai karancin Malamai da azuzuwa da sauran su. Sanadiyar haka ne yasa Dr. Mansur ya fara aiwatar da shawarwarin da aka gabatar masa ta hanyar farawa da daukan malamai.
Dr. Mansur yace wannan soma tabi ne da zarar an zabe shi, zai aiwatar da dukkan shawarwarin da ya samu daga al'umman Dandi.

Manya baki da suka sami damar halartan wannan taron sun tofa albarkacin bakin su:
 A jawabin sa,  jigo a Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Umar Idris Buro wanda Kabiru Labbo (Ajiyan Jega) ya wakilta yace " mutanen karamar hukumar mulki ta Dandi ku rike DR. MANSUR ina mai tabbatar ma ku cewa tabbas kunyi dace da shugaba a karamar hukuma haziki, ma ilmanci. Dr. Mansur  ya zo ne kawai bisa umarni don Kuma ya taimakawa al'umma amma ba saboda satar kudin gwamnati ba, domin tuni Allah Ya azurtashi" 

A jawabin sa Shugaban Karamar hukumar Dandi  DR. MANSUR ISAH KAMBA ya bayyana cewa a baya daga cikin gudunmuwar da ya bayar a fannin Ilimi ga matasan Dandi ciki hadda raba JAMB forms kyauta ga dinbin matasa  domin samu guraben karatu a makarantun gaba da sakandare wanda dalilin haka da yawa sun samu sun kammala karatun wasu kuma sunanan sunayi a halin yanzu .
 
" Idan ka taimaki mutum yayi karatu Yana da kyau ka Kuma taimaka masa ya samu aiki, don haka yanzu damace a gare ni in taimaka ma wayannan matasa da aikin yi" inji Dr. Mansur a lokacin da yake bayarda da takardar daukar aiki ga sama da Matasa 100 da ya dauka aiki.
Sarakuna, Yan siyasa da manyan ma'aikatan Gwamnati na jiha da na karamar hukuma ne suka halarci wannan taron.

Post a Comment

0 Comments