Sabuwar Karamar Hukumar Dandi
Sabuwar Karamar Hukumar Dandi
" Zan Zama Shugaban Karamar Hukumar Dandi Na Farko Da Zai Gayyato Gwamna Domin Kaddamar Da Ayukkan Raya Kasa A Dandi" Inji Dr. Mansur Isah
By Ahmad Umar
Shugaban Karamar Hukumar Dandi, Dr. Mansur Isah Kamba yace zai kafa tarihi na zama shugaban Karamar Hukumar Dandi na Farko da Zai Gayyato Gwamna domin kaddamar da ayukkan ci gaban kasa a karamar hukumar Mulki ta Dandi.
Dr. Mansur yayi wannan alwashin ne a lokacin da yake ganawa da jaridar Kebbi-Trust
Yace tuni ya riga ya tantance ayukkan da zai aiwatar cikin shekara daya na farko na shugabancin sa.
Idan za a tuna a watan mayu na 2024 ne Dr. Mansur yayi zagaye a dukkan fadin wards 11 dake karkashin karamar hukumar Dandi, inda Yaba mutanen kowace ward da su fadi irin ayukkan da suke so karamar hukuma tayi masu.
Dr. Mansur yace an kammala tantancewa da hada alkalumma da ake bukata domin fara aiwatar da aiki wuri-jam-jam babu kama hannun yaro.
Yace idan aka kammala ayukkan kamar yadda aka tsara zai Gayyato Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu domin ya kaddamar da ayukkan In Sha Allah.
Ga kadan daga cikin mummunan halin da wasu gine ginen Gwamnati suke ciki a a Dandi wayanda Dr. Mansur yasha alwashin gyarawa cikin shekara daya akan milki idan Allah Ya yarda:
Post a Comment
0 Comments