Waya Karya Umurnin Kauran Gwandu?
Waya Karya Umurnin Kauran Gwandu?
Karon Farko A Tarihin Jihar Kebbi An Ki ba Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Kayan Abinci
A bisa al'ada a duk lokacin da Gwamnatin Jihar Kebbi ta rabawa ma'aikatanta kayan abinci takan hada da takwarorin su ma'aikatan Gwamnatin Tarayya dake aiki a Jahar Kebbi.
Gwamnatin da ta gabata ta Atiku Bagudu tafi fice wajen kulla wannan zumunci domin duk irin wannan lokacin sai ta rabawa ma'aikatun Gwamnatin Tarayya Shinkafa, Gero, Masara, Suga, Shanu ko kudin sayen Shanu.
Duk ma'aikatan Gwamnatin Tarayya dake da ofis a Jahar Kebbi sai sunga wannan alherin lokacin Dan-Bagudu a irin wannan lokacin na azumi.
Kuma wannan al'adar tun kirkiro Jihar Kebbi haka akeyi sai wannan karon aka samu akasi inda aka sabawa wannan al'adar, a lokacin Gwamnan da akewa shaidu da yawan kyauta da alheri.
Bayan haka, Gwamnan Jihar Kebbi maici yanzu Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) yafi duk wani Gwamna da akayi a Jihar Kebbi kusanci da alaka da ma'aikatan Gwamnatin Tarayya la'akari da cewa ya riki mukamin mataimakin shugaban kwadago na kasa.
Abin mamaki shine a lokacin da Gwamna Jihar Kebbi Dr Nasir Idris ke kaddamar da rabon kayan a ranar Alhamis 21/ 03/2024 anji shi Yana cewa, wasu sun bada shawaran kada aba ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, amma ya tabbatar wa taron cewa bai karbi wannan shawaran ba, bisa hujjan cewa Suma Jihar Kebbi sukewa aiki, " Don haka na umurci a hada da ma'aikatan Gwamnatin Tarayya a basu wayannan kayan abincin" Inji Gwamna Nasir Idris
Yanzu dai an raba kaya an gama, ma'aikatan Gwamnatin Tarayya sun tashi tsula:
TAMBAYA:
Wa ya Karya Umurnin Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu?
Ko Gwamna ne yayi amai ya lashe, ta hanyar janye umurnin da ya bayar tun farko?
Ko kayan abinci ne sukayi karanci?
Ko mukarabban da tun farko suka bada shawaran kada aba ma'aikatan Gwamnatin Tarayya kayan ne, suka nace akan ra'ayin su duk da umurnin da Gwamna ya bayar?
Ko layi ne bai kawo ga ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ba?
Lokaci ne zai amsa wayannan tambayoyi, domin wannan kuskuren ba karamin illa bane ga wannan gwamnati da ake cewa ba asanta da rowa ba.
Post a Comment
0 Comments