Hon. Halima Tayi Kira Ga Matasan Kebbi Su Zama Masu Da'a
JAHAR KEBBI, JAHAR ZAMAN LAFIYA, TARBIYA, KWANCIYAR HANKALI DA BIYAYYA GA SHUGABANIN CE__Inji Hon. Halima Hassan Yauri
Tsohuwar Yar' majalisar wakilai data wakilci kananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski a majalisan wakilai ta kasa, kuma mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Yauri, har ila yau kuma Babban Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara ta Musanman; Hon. Halima Hassan Tukur Yauri( Jarumar mai martaba Sarkin Yauri) tayi Allah waddai da tabi'un wasu bara gulbin matasa da suka fasa rumbum ajiyar kayan abinci Gwamnati da na yan'kasuwa inda suka ya sashe kayan abinci mai dimbin yawa.
Hon. Halima ta nuna alhini da jajantawa dukkan wayanda lamarin ya shafa.
Tace ba asan yan asalin Jihar Kebbi ba da irin wannan mummunar tabi'a
"Amma kome ya bata tarbiyan wasu ya'yan mu har suka balle ma'adanin abincin Gwamnati da na Yan kasuwa suka saci kayan abinci, wannan ba tarbiyar matasan Kebbi bane" ta bakin Hon. Halima
Tayi kira ga Gwamnatin Jiha da ta kirkiro da hanyar tantance baki musanman daga kasashen mukwabta dake shigowa Jihar Kebbi domin kawar da bata gulbi kafin su bata matasan Kebbi da aka sani da da'a da biyayya.
Hon. Halima tayi kira ga al'ummar jahar kebbi su Kara hakuri Kuma su Kara baiwa gwamnati goyon baya domin Karin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali acikin jahar.
Haka kuma tayi kira ga iyaye da su Kara saka idanu da Kuma Kara Jan kunnen yaransu musamman matasa domin su zamo jakadu nagari, masu kare martabar jahar su ta Kebbi ba masu zubar mata da daraja ba.
"Mu Kara baiwa gwamnatn Dr.Nasir Idris Kauran Abdullahin Gwandu, Gamjin Yauri goyon baya domin ta samu damar ci gaba da ayyukan alherin da fara don ci gaban jaharmu" Inji Hon. Halima Hassan Tukur Yauri.
Post a Comment
0 Comments