An Yabawa Kantoman Karamar Hukumar Dandi

MUTANEN KARAMAR HUKUMAR DANDI SUN YABAWA KANTOMAN SU, DR. MANSUR ISAH KAMBA BISA KOKARINSA NA DAWOWA DA WUTAN LANTARKI A KARAMAR HUKUMAR.

Bayan daukewar wutan lantarki a garin Kamba da sauran garuruwan dake cikin karamar hukumar mulki ta Dandi, sanadiyar karewar daya daga cikin chaben dake dauke da wutan daga Birnin Kebbi a garin Bunza, wanda yayi sanadiyar daukewar wutan a garin Kamba da sauran garuruwan dake wajen Kamba.
Bayan sanar da shi halin da ake ciki, Kai tsaye Kantoman ya tayar da tawaga na wakilai zuwa Birnin Kebbi domin yin abinda ya kamata.

Bayan matsayar da aka cimma da  ma'aikatan wutar lantarki na jihar Kebbi akan wannan matsalar Kai tsaye Dr. Mansur  ya bada umarni da kayan aiki, aka dauko hayar motar daukan chabe daga Birnin Kebbi, aka zo Kamba aka dauki chaben da aka tanadar don irin wannan matsalar, akaje Bunza aka gyara matsalar.
Bayan kammala aiki kai tsaye wutan Lantarki ta dawo a garin Kamba da Kewaye, wannan ne yasa al'umma karamar hukumar Mulki ta Dandi musanman kungiyar 'Concerned Citizens Dandi Local Government' da sauran kungiyoyi da al'umma yabawa Dr. Mansur Isah bisa daukar matakin gaggawa wajen dawo da wutan lantarki a karamar hukumar Dandi.

Post a Comment

0 Comments