Abin Mamaki A Nijeriya

*Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bayar Da Kwangila Gina Hanya Daga Lagos Zuwa Calabar Akan Naira Tiriliyan 15 (N15 Trillion)* 

A wani al'amari mai daure kai Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da aikin gina hanya ta zamani da zata ratsa jahohin kudu har 9 akan zunzurutun makudan kudade da suka kai Naira Tiriliyan 15 (N15 Trillion) kusan rabin kasafi kudin Nijeriya kenan

Jahohin kudu da aka tsara zasu anfana da wannan ayukkan sun hada da Lagos,Ogun,Ondo,Delta,Edo,Bayelsa,Rivers, Akwa Ibom,Cross River, ma'ana titin duk sai ya ratsa wayannan jahohin

An tsara gina Otel,Asibiti, da sauran ababen more rayuwa akan wannan titin kamar yadda na kasashen turai su ke.

Tuni dai shugaba Tinuba yabada umurnin biyan diya ga dukkan wayanda za a taba filaye ko gidajen su domin aiwatar da aikin kamar yadda ministan ayukka Mr. David Umahi ya tabbatar.

TUNA BAYA: KO DATTAWAN AREWA ZA SU KOKA?

Idan mai karatu zai tuna a lokacin Mulkin Shugaba Muhammad Buhari, aikin hanya Mafi tsada da cin kudi da ya bayar itace hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano akan kudi kusan Naira Biliyan 800 (N800Billion) ma'ana ko Naira Tiriliyan daya (N1 trillion) basu kai ba..

Amma sai da DATTAWAN KUDU suka koka suka ta Kiran 'meeting' a tsakanin su, dakyar ministan ayukka na wancan lokacin Babatunde Fashola Wanda shima dan kudu ne yaciyo kansu akancewa idan aka hada ayukkan hanyar da akeyi a kudu sunfi na Arewa yawa da cin kudi tun a wancan lokacin, akan haka suka hakura, aka ci gaba da aikin.

Yanzu ana zance NAIRA TIRILIYAN 15 ko DATTAWAN AREWA za suyi koyi da takwarorin su na kudu ta hanyar kokawa akan wannan ha'inci da akawa Arewa?

Kalu bale ga Yan majalisu da Sanatoti da sauran dattawan Arewa.

Post a Comment

0 Comments