KAURAN GWANDU YA NADA KAURAN YAURI

KAURAN GWANDU YA NADA KAURAN YAURI
MURNA TA BARKE A GARIN YAURI, BAYAN MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KEBBI DR. NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU) YA NADA ABUBAKAR SHU'AIBU (KAURAN YAURI) A MATSAYIN SHUGABAN RIKO NA KARAMAR HUKUMAR YAURI  


Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya nada matashin dan kasuwa Kuma dan siyasa mai farin jini Alhaji Abubakar Shuaibu da akafi sani da Abu Manaja (Kauran Yauri) a matsayin Shugaban riko na karamar Mulki ta Yauri.

Wannan nadin ya farantawa Yawurawa da dama rai kasancewar Abu Manaja mutumin mutane ne dake da kyakkyawan ma'amala da kowa.

Kauran Yauri fitaccen dan kasuwa ne kuma dan siyasa da ya dade yana biyayya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi, kuma ya taka rawar azo a gani wajen tabbatar da samun nasaran cin zaben Kauran Gwandu a masarautan Yauri a zaben 2023 da ya gabata.
Kauran Yauri matashi ne mai yawan alheri da kyauta, bai  wasa da addini, ga saukin kai,kuma kamilin dattijo ne mai mata  4.

Kamar yadda Kauran Gwandu a matsayin sa na Gwamnan Jihar Kebbi Yake watsa ayukkan alheri a fadin Jihar Kebbi, haka ake  kyautata zaton Kauran Yauri zaiyi ayukkan alheri, a matsayin sa na shugaban riko na Yauri da ake sa ran Kuma ya zama zababben shugaban karamar hukuma Mulki ta Yauri In sha Allah.
_________________________

07038182929

Post a Comment

0 Comments