Kaura Ya Aikata Aikin Sa Na Alheri

ISKOKAN ALHERI SUN MOTSA A JIHAR KEBBI: KAURAN GWANDU YAYI HALIN SA 
- Ya bada umurnin biyan ma'aikatan Gwamnati Albashi daga yau Alhamis 21/03/2024

-Ya bada umurnin biyan kudin hutu na ma'aikata

-Ya bada umurnin biyan kudin ritaya ko rasuwa cikin wata daya

-Ya bada umurnin raba kayan abinci na biliyoyin naira

- Ya dinkawa manyan sarakunan Gargajiya 4 Manyan Riguna Na Alfarmar Har Guda 960

-Ya sha alwashin ci gaba da manyan ayukka na gina kasa a ko ina a fadin Jihar Kebbi

Ance mai hali baya barin halinsa; Babban halin da kowa ya shaidi Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) shine ALHERI, Kuma ga dukkan alamu bai da niyar barin wannan kyakkyawan halin.

A ranar Alhamis 21/03/2024 ga ayukkan alheri da ya aikata a Jihar Kebbi:

- Umurnin tallafin kayan abinci

A yau Alhamis 21/03/2024 mai girma Gwamna Jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya kaddamar da  rabon tallafin dubban buhuhuwa na kayan abinci na biliyoyin naira da suka hada da Shinkafa, Gero, Masara da sauran su, Wanda za a raba a ko'ina a fadin Jihar Kebbi.
- Umurnin biyan Albashi

Bayan kayan abincin, Gwamnan ya bayar da umurnin fara biyan Albashin ma'aikata na jiha da kananan hukumomi daga yau Alhamis 21/ 03/2024.
- umurnin biyan kudin hutu

Gwamna Idris ya Kuma bayar da umurnin biyan kudin hutu tun yanzu a watan 3 maimakon watan 12 da aka saba
-umurnin biyan kudin ritaya ko rasuwa

Har ila yau Gwamna ya bayar da tabbacin biyan duk wani ma'aikaci da yayi ritaya ko ya rasu dukkan hakinsa cikin tsawon wata daya tak, sabanin da Inda ma'aikaci ke share shekaru yana jiran hakkin sa bayan yayi ritaya
- Dinkawa Manyan Sarakunan Gargajiya 4 Dake Jihar Kebbi kayan sallah

Kauran Gwandu, ya rabawa manyan masarautun jihar su 4, manyan riguna na alfarmar guda 960. 

 Ma'aikatar Kula da kananan hukumomi da masarautan jiha ne suka gabatar da kayyakin  wayanda aka kunsa su cikin buhuhuna 16 na tufafi, kowanne buhu na dauke da kala 60. 

 Masarautar Gwandu ta samu buhu 6, Argungu buhu 4, Yauri buhu 3, sai Zuru itams tasamu buhu 3.

- Alwashin ci gaba da manyan ayukka

Kauran Gwandu yace wayannan hidimomin da kyautatawa da yakewa al'umma bazasu shafi manyan ayukkan da yake aiwatar waba a fadin Jihar Kebbi da iKon Allah.
 
KAURA YA BADA UMURNIN BIYAN KUDIN NECO DA WAEC KUSAN NAIRA BILIYAN DAYA..
_____________________________
ahmadugamji@gmail.com
07038182929

Post a Comment

0 Comments