BUHARI BALA YA SAMARWA MATASAN KEBBI AIKI
Tsohon Minista Buhari Bala ya baiwa matasa da dama aiki a Jihar Kebbi
Sabon Gidan Radio mallakin Alhaji Buhari Bala, tsohon Ministan harkokin kasashen waje, watau NAGARI RADIO 88.7 FM ya dauki dimbin matasa wadanda suka hada maza da mata aiki.
Ma'aikatan sun hada da masu gabatar da shirshirye (Presenters/Announcers), da masu nemo labarai (Reporters), da masu gabatar da shirye-shirye na musanman a bangarorin rayuwar jama'a da suka hada da fannin noma, ilimi, lafiya, kasuwanci, tarihi, wasanni da sauran su.
Da yake ganawa da sabbin ma'aikatan, babban manajan gidan radio Iliyasu Abubakar ya umurci sabbin ma'aikatan da su kasance masu da'a da sanin ya kamata kamar yadda dokokin aikin jarida suka tanadar a lokacin da suke aiwatar da aikin su.
Ilyasu Abubakar yace babban burin Nagari Radio shine bayar da gudumuwa domin kawo fihinta tsakanin shugabanni da talakawan su da kuma wayar da kan jama'a musanman manoma domin inganta harkokin noma da Jahar Kebbi tayi fice akai.
Anasa ran NAGARI RADIO zai fara gabatar da shirye shiryen sa a cikin wannan watan na Fabarairu, 2024 akan mita 88.7.
_________________________________
GYARA KUSKURE: Nagari Radio Yana akan mita 88.7 ne ba 88.9 ba.
A kwanakin baya wanna kafan yada labarai ta Kebbi-Trust ta bada labari akan wannan Sabon gidan Radio na Nagari, a harshen turanci, a wancan labarin anyi kuskure akan mitar da Nagari Radio ke yada labarai, Inda aka rubuta 88.9 bisa kuskure. NAGARI RADIO Na akan mita 88.7 ne. Sai ayi muna afuwa.
Post a Comment
0 Comments