SIYASAR YAURI/SHANGA/NGASKI 2024
SIYASAR YAURI/SHANGA/NGASKI 2024
ZABEN CIKE GURBI: Duk Dan-Takaran Da Bai Fadi Ayukkan Da Zaiyi Ba Kada A Zabe Shi: __Inji Kungiyar Masu Kishin Masarautar Yauri
Kungiyar Masu Kishin Masarautar Yauri (Yauri Emirate Patriots) tayi kira ga mutanen kasar Yauri da cewa duk wani dan takaran kujeran majalisan wakilai da bai fito filiba ya bayyana ayukkan da zaiyi wa jama'a kada a zabe shi.
Shugaban kungiyar na riko Alhaji Arzika Yauri, yace kungiyar su ta fahinci wasu yan takaran basu ma san dalilin da yasa suka fito takaran ba, wasu Kuma sun fito ne don azurta kawunan su kawai.
Kungiyar ta bayyana cewa Babban Kuskuren da Yawurawa za suyi shine zabe cikin duhu, ma'ana a zabi mutum ba tare da ya fadi irin ayukkan da zai aiwatar ba, ko Kuma zaben mutumin da ake zargi da wawure dukiyar Yawurawa.
Da karshe kungiyar ta bayyana cewa zata fito kirikiri ta goyi bayan dukkan dan takaran dayafi manufofi da zasu kawo wa Masarautar Yauri da al'ummata ci gaba.
Idan za a tuna, Wanda ke kan kujeran majalisan wakilai da ke wakiltar Yauri/Shanga/Ngaaki Hon. Dr. Tanko Yusuf Sununu ya sami daukaka zuwa kujeran Minista, Wanda yabar gurbin da ake kokarin cikawa a yanzu. Tuni hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ayyana 4/2/2024 a matsayin ranar da za ayi zaben cike gurbin. Kuma tuni Yan takara daga jam'iyar APC da PDP da sauran jam'iyu suka nuna shawan su na maye gurbin Dr. Tanko Sununu.
_________________________
HON. HALIMA HASSAN TUKUR YAURI (JARUMAN MAI MARTABA SARKIN YAURI) TA AMSA KIRA TA BAYYANA AYUKKAN DA ZATA AIWATAR IDAN AKA ZABE TA:
Hon. Halima ta banbanta kanta da sabbin yankan raken siyasa, wayanda ke takara amma basu San dalilin da yasa suke takaran ba .
A halin yanzu itace kawai ta bayyanawa Yawurawa ayukkan alherin da zata aiwatar idan aka zabeta.
Ta bayyana kudorori 8 (8 points Agenda) kamar haka:
1- Jajircewa wajen samarwa matasa Maza da mata ayukkan Yi a ma'aikatun Gwamnatin tarayya, kamar yadda tayi a baya
2- Gina wuraren koyon sana'o'in hannu domin koyawa jama'a sana'o'i da kuma basu jari domin dogaro da kai
3- Jagoranci zuwa ga bankin manoma(Bank of Agriculture) da Bankin masana'antu (Bank of Industry) da sauran su domin samarwa Yawurawa bashi marasa ruwa da zai Inganta kasuwancin su da Kuma haddasa kafuwan kamfuna a Yauri.
4- Jajircewa domin tabbatuwar Tashan jiragen ruwa ta zamani a Yauri ( Yauri Wharf)
5- Jajircewa domin kawo kanfanin sarrafa zinari a Yauri
6- Bayar da taimako Kai tsaye zuwa ga Masu sana'o'in hannu kamar Masu tireda, masunta, direbobi(NURTW) Yan Kabu-kabu da sauran su, domin Inganta sana'o'in su.
7- Taimakawa Kai tsaye a fannin ilmi da kiyon lafiya ta hanyar gyara da gina makarantu da Asibitoti kamar yadda akayi a baya
8- Bayar da taimako Kai tsaye ga sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro irin Yansanda, civil defense da sauran su domin Inganta tsaro da zaman lafiya a masarautar Yauri baki daya
Yanzu shawara naga Yawurawa ko suyi zabe don ci gaban Masarautar Yauri ko subi son zuciya suyi zabe don azurta dan takara da iyalin sa.
Post a Comment
0 Comments