NAFISA NASIR IDRIS ZATA KAFA TARIHI
NAFISA NASIR IDRIS ZATA KAFA TARIHI
MATAR MAI GIRMA GWAMNAN JAHAR KEBBI HAJIYA NAFISA NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU) ZATA KIRKIRO RANAR TUNAWA DA MATA MASU LALURAN YOYON FITSARI, TA KUMA YI SHIRI NA MUSANMAN DOMIN KAWAR DA CUTAR A JIHAR KEBBI
A ci gaba da kokarin da ta keyi na kawar da cutar yoyon fitsari a fadin Jahar Kebbi, Matar Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Nafisa Nasir Idris (Kauran Gwandu) na Shirin kirkiro da rana ta musanman domin tunawa da mata Masu laluran yoyon fitsari (KEBBI FISTULA DAY) a karon farko a tarihin Jahar Kebbi.
Ma'ana wannan gangami da take kokarin gayyatowa shine irin sa na farko a Jahar Kebbi.
Tuni shirye shirye su kayi nisa tsakanin Gidauniyar ta NANAS Foundation da kungiyar FISTULA CARE KEBBI dake da masana da kuma shahara wajen kawo masalaha akan cutar yoyon fitsari.
An tsara gudanar da wannan gangami a wata Disimba na wannan shekaran (December,2023).
Ana sa ran gayyato mutane musanman mata daga ko Ina fadin Jihar Kebbi domin wayar Masu da kai akan cutar yoyon fitsari.
Masana da kwararrun likitoti akan wannan cutar zasu hallaci gangamin domin ilimatar da jama'a akan laluran yoyon fitsari.
SHIRIN ZAKULO MASU LALURAN YOYON FITSARI DON KAWO SU ASIBITI
Bayan wannan gangami an tsara Gidauniyar NANAS Foundation da kungiyar FISTULA CARE KEBBI zasu zagaya dukkan birane da kauyukkan dake fadin Jihar Kebbi domin Zakulo Masu wannan laluran don kawo su Asibiti don a warkar da su.
Hajiya Nafisa Nasir Idris ta tsara shirye shirye na musanman da za a dinga gabatarwa a gidajen watsa labarai da suka hada da Radio, Tv da sauran su.
Har ila yau za a wallafa kasidu da manyan alluna (Billboard) domin wayar da kan jama'a akan wannan cutar da Kuma matakin da ya kamata a dauka tare da bayani akan Asibitin da za a je idan an kamu da wannan cutar.
Tuni dai aka fara yada sakonnin baka (Radio/TV jingles) duk akan wayar da kan jama'a musanman mata akan wannan laluran ta yoyon fitsari.
Post a Comment
0 Comments