LAFIYAR YA'YA MATA

LAFIYAR YA'YA MATA

MATAR GWAMNAN JAHAR KEBBI HAJIYA NAFISA NASIRU IDRIS TASHA ALWASHIN KAWAR DA CUTAR YOYON FITSARI A TSAKANIN YA'YA MATA A JAHAR KEBBI__TAYI KAWANCE DA KUNGIYAR NGO MAI SUNA 'FISTULA CARE KEBBI' DOMIN SAMUN NASARA

Daga Ahmad Umar

Matar Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Nafisa Nasiru Idris tasha alwashin yin duk abinda ke yiwuwa domin kawar da cutar yoyon fitsari da ake kira atakaice da turanci VVF, a tsakanin Ya'ya mata a dukkan fadin Jahar Kebbi.

Hajiya Nafisa ta dauki wannan kuduri ne a ranar Talata 19/09/2023 a Lokacin da take ganawa da wata Kungiya Mai zaman kanta (NGO) Mai suna FISTULA CARE KEBBI da ta shahara wajen kawo masalaha akan cutar yoyon fitsari da makamantar su karkashin jagorancin Dr. Muhammad Yusuf.

Shi dai ciyon yoyon fitsari wata tsaguwane dake faruwa a gaban mata da ke haifar da fitar fitsari ba kakkautawa.

Babban abinda ke janyo wannan cutar sune tsohuwar al'adar yankan gishiri ko yankan gurya da kuma doguwar nakuda da mata keyi yayin haihuwa.

Tsaguwa a gaban mata ko Kaba da Kuma Jin zafi yayin saduwa na kadan daga cikin alamomin da idan macce taji su, sai ta hanzartar sanar da hukuma domin Samar mata da mafita, domin cutar yoyon fitsari abine da ake iya maganin sa ya warke tsaf.

Hawaye sun kusan cikawa Hajiya Nafisa idanuwa Lokacin da Dr. Abdullahi Hussaini Babban jami'i a Shirin da ake kira da turanci, MOMENTUM Engender health project da Kuma Dr. Amina Usman Bello shugaban Asibitin VVF ta Jahar Kebbi suke baiwa Matar Gwamna labarin mummunan halin da wayanda suka kamu da cutar yoyon fitsari ke samun Kansu, da suka hada da tsangwama, damuwar kwakwalwa da kawar duk fatan na gari.

Bisa wannan ne Matar Gwamna tasha alwashin zama uwa ga dukkan wayyanda suka kamu da wannan cutar ta hanyar taimaka masu har sai sun warke.

Ta Kuma yi alkawalin Samar da ingantaccen wutan lantarki Mai anfani da hasken rana 'Solar Energy ' da Kuma gyara dakin koyon sana'o'i da ke cikin Asibitin VVF dake Birnin Kebbi.

Har ila yau, Hajiya Nafisa tayi alkawalin bayar da dukkan gudumuwar da ake bukata domin Samar wa Ya'ya mata da jarirai ingantaccen lafiya a dukkan fadin Jahar Kebbi.

GUDUMUWAR DA KUNGIYAR NGO 'FISTULA CARE KEBBI' ZATA BAYAR

Da yake jawabi a madadin kungiyar FISTULA CARE KEBBI, Babban jami'i a Shirin da ake kira da turanci 'MOMENTUM Engender health project' Dr. Abdullahi Hussaini ya bayyanawa Hajiya Nafisa cewa kungiyar na bukatar hadin kanta domin aiwatar da tsare tsare da za su bayar da damar samun nasaran kawar da cutar yoyon fitsari a Jahar Kebbi baki daya.

Ya bayyana cewa kungiyar FISTULA CARE KEBBI ta tsara ayukkan wayar da kai da ilmantar da jama'a akan cutar yoyon fitsari domin zakulu Masu cutar zowa Asibiti domin a warkar da su.
Dr. Abdullahi Hussaini ya ce shirye shiryen sune:

1- WAYAR DA KAWUNAN JAMA'A: Kungiyar ta tsara ziyarta dukkan manyan masarautun dake fadin Jahar Kebbi da Kuma Shugabanin al'umma.

2- ILMANTAR DA JAMA'A: Kungiyar ta tsara wallafa manyan allunan wayar da kai watau Billboards, kasidu, wakoki, sakon baka da Kuma tsara shirye shiryen ilmantar wa akan VVF a gidajen Radio da Television.

3- ZIYARAR FADAKARWA: Kungiyar FISTULA CARE KEBBI, ta tsara ziyarta dukkan masu ruwa da tsaki kamar Shugabanin addini, da na al'umma da kuma sarakunan gargajiya

4-KIRKIRU DA RANAR TUNAWA DA MASU YOYON FITSARI: Kungiyar ta tsara yin gangami tare da taron wayar da kai, Inda za a raba kasidu Masu ilmantar wa akan cutar yoyon fitsari.


MATAR GWAMNA TA AMINCE DA KUNGIYAR FISTULA CARE KEBBI TARE DA BASU UMURNIN FARA AIKI KAI TSAYE

Kai tsaye Hajiya Nafisa taba Kungiyar FISTULA CARE KEBBI umurnin fara aiwatar da tsare tsaren da suka shirya musanman sakon baka (jingles) da za a sanya a gidajen Radio da Television da sauran ayukkan wayar da kai da kungiyar ta tsara aiwatar wa domin Kai sako a dukkan sako da lungun dake fadin Jahar Kebbi.

Tayi alkawalin bayar da gudumuwa da aiki tare da kungiyar FISTULA CARE KEBBI domin samun nasaran kawar da cutar yoyon fitsari (VVF) a Jahar Kebbi.

A wannan ganawar ta musanman da kungiyar FISTULA CARE KEBBI, Matar Gwamna, Hajiya Nafisa Nasiru Idris (Kauran Gwandu) ta Sami rakiyar Matar Sakataren Gwamnatin Jahar Kebbi, Hajiya Asma'u Alkali da sauran Shugabanin kungiyoyin mata a Jahar Kebbi.

Post a Comment

0 Comments