Malami Ya Zama Dan Shugaban Kasa

CI GABA: Malami Ya. Zama Dan Shugaban Kasa

Liyarfar Ministan Shari'a na Najeriya, Babban Lauya Abubakar Malami ta sake tashin gwauron zabo, inda ta haye zuwa sararin samaniya.

Bayan amincewar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi masa ta hanyar bashi mukamin Minista, mafi girma da daraja har na tsawon shekaru 8, sai gashi kuma ranar juma'a 9-Zul-Hijja, 1443AH daida  8/7/2022, Shugaba Buhari ya yiwa Abubakar Malami rajistan zama dan sa mai-tuta ta hanyar auran masa da diyar sa HAJIYA NANA HADIZA MUHAMMADU BUHARI.

A al'adan Hausa/Fulani duk Wanda ya baka diyar sa aure, ya zama tamkar uba, kai kuma ka zama tamkar da a wajen sa. Bisa wannan dalilin za a iya cewa Minista Abubakar Malami ya zama da a wajen Shugaba Buhari.

Yanzu dai Abubakar Malami ya zama kamilin Dattijo ta hanyar mallakar mata 3, da suka hada da AISHA, FATIMA da Kuma Amarya NANA-HADIZA.

Jaridar kebbitrust na taya Ministan Shari'a murnan samun wannan daukaka da addu'ar Allah Ya bada zaman lafiya da zuriya mai albarka da al'umma za suyi alfahari da su.

Post a Comment

0 Comments