Taimakon Malami a Zuru


GUDUMMAWAR MINISTAN SHARI'A KUMA BABBAN LAUYAN GWAMNATIN TARAYYA ABUBAKAR MALAMI SAN, GA AL'UMMAR DA TA'ADDANCI YA ADDABA A YANKIN ZURU.


Idan dai baku manta ba  yankin masarautar Zuru da Yauri na daya daga cikin yankunan da ke fama da hare- haren barayin daji wato Yan bindiga.
Akan hakan ne acigaba da kokarin da yake yi na bayarda ayukkan jinkai ga al'ummar da iftilain ya sama,  Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar Najeriya Abubakar Malami SAN ya bayar da gudummawar kayan abinci na kimanin buhun shinkafa ɗaru bakwai da kuma  hatsi da masara  domin rabawa sansanonin ƴan gudun Hijira dake akwai a wannan yankin na Zuru.


Adai gudanarda taron bayarda gudumuwar buhuhuwan ne a fadar Mai martaba Sarkin Zuru inda Mai girma Minister da Kansa ya jagoranci bayarda gudumuwar.


Dayake jawabi ayayin taron karbar gudumuwar amadadin al'ummar yankin Zuru Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami na II ya bayyana Abubakar Malami SAN amatsayin mai kishin ƙasa wanda ya tabbatar da cewa shi ɗan Masarauta Zuru ne na gaske wanda ke da alaƙar da al’ummar Masarautar. 


Abubakar Malami SAN, bai tsaya anan ba domin ko a watan Ramadanan da ya gabata sai da ya  raba shinkafa da kayan masarufi wa ƴan gudun Hijira a ƙaramar hukumar mulki ta Danko-Wasagu, Sakaba  da wasu sassa na ƙananan hukumomin Zuru.

Har wayau Minister Shari'a Abubakar Malami SAN, ya tura wata babbar tawaga akarkashin jagorancin Shugaban kwomitin Amintattu na Gidauniyar Khadimiyya Abubakar Usman Gotomo inda tawagar ta kai taimakon gaggawa a garin Ribah.

Kayayyakin da tawagar ta kai sun hada da Turame na mata, Shadda, Sabulun wanki, Sabulun wanka, Man gyada, Magi, Gishiri hadi da tabarmi.


Haka zalika ko a shekaranjiya  ranar 14 na wannan wata, ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu goyon bayan Abubakar Malami SAN ta Malami Alliance for Women Development (MALAWOD) ta raba shinkafa da tabarmi ga wasu daga cikin waƴanda harin ƴan ta'adda ya shafa ayankin Zuru.

Ahmad Usman Mairukubta
Jami'in Tattara Bayanai na Gidauniyar Khadimiyya.

Post a Comment

0 Comments