Politics
ATIKU BAGUDU DA ADAMU ALEIRO SUN SAKE HADUWA
Gwamna Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aleiro Sun Ziyarci Kaduna Tare.
www.kebbitrust.com
Shugaban Gwannonin Jam'iyar APC na kasa Senator Abubakar Bagudu tare da Sanata Adamu Aleiru da Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Sa'idu Nasamu Dakin Gari tsohon Gwannan zamfara Ahmed Sani yariman Bakura sun Kaiwa gwamitin Jihar Kaduna jaje akan iftila'in da ya faru na Harin jirgin kasa a ranar littinin 28/3/2022.
A yayin ziyaran sun jajantawa gwamnati da kuma al'ummar jahar Kaduna tare da rokon Allah da kare aukuwar wannan iftila'i.
Wani abin da ja hankalin jama'a musanman jama'ar jahar Kebbi shine yadda Gwamna mai ci Atiku Bagudu yaja Yayansa Sanata Adamu Aleiro zuwa Kaduna domin wannan jajen.
Ranar Jama'a da ta gaba wannan jaridar ta yanan gizo ta kawo wa masu karatu ziyaran bazata da Sanata Adamu Aleiro ya kaiwa kanin sa Ministan Shari'a Abubakar Malami a gidan sa dake Abuja.
Binciken da jaridar Kebbitrust ta gudunar game da wannan fahintar juna da ake samun tsakanin wayannan jigogin siyasar Kebbi ya nuna cewa talakawan jahar Kebbi na murna da wannan sabon abutta, sai dai wasu yan siyasa basu murna da haka, bisa tunanin su cewa sai manya na fada zasu sami na sakawa aljihu.
"Muna fatar wannan fahintar zata daure, muna rokon Allah Ya kara hada kawunan wayannan shugavannin namu, ya zabar muna mafi alheri" Inji Kabiru A. Ibrahim Masama, wani talaka a Birnin Kebbi.
Post a Comment
0 Comments