A KARRAMA MUHAMMADU KANTA: SHAWARA GA MAGABATAN JAHAR KEBBI


A KARRAMA MUHAMMADU KANTA: SHAWARA GA MAGABATAN JAHAR KEBBI


La'akari da gudumuwar da Marigayi Sarkin Kebbi na Farko Muhammadu Kanta ya bayar wajen kafuwar Daular Kebbi (Kebbi Empire) ya dace ace a sanyawa wata babban ma'aikata ko makaranta sunansa, kamar yadda aka karrama Sarkin Gwandu Marigayi Sir. Yahaya ta hanyar sakawa babban Asibitin Birnin Kebbi sunansa (Sir Yahaya Memorial Hospital), da kuma yadda aka karrama tsohon Wazirin Gwandu da Waziri Umaru Federal Polytechnic, Birnin-Kebbi da Sarki Haliru Abdu da sauran su.

WANENE MUHAMMADU KANTA?

Muhammadu Kanta ko Kanta Kotal zarumine da akewa kirari da ' Kai kadai Gayya' Janar ne na soja a rudunar sojojin daular Songhai (Songhai Empire) karkashin shugabanci Askiya Muhammad.

Kanta shine ya jagoranci yakin da aka ciyo manyamanyan kasashen Hausa da suka hada da Kano, Gobir, Katsina, Zazzau da Zamfara har zuwa Agadez dake kasar Nijar a Yanzu.

Bayan kammala wayannan yake yake sai Kanta yaga ba ayi mishi adalci ba wajen rabon ganimar yaki, don haka sai yayiwa daular Songhai tawaye ya cire yankin Kebbi daga Songhai ya mayar da ita daula Mai zaman kanta inda ta zama KEBBI EMPIRE kuma ya nada kansa a matsayin sarki na farko na Daular Kebbi. 

Daular Songhai basu barwa Allah ba, sunyi ta kawo hare hare domin sake mayar da Kebbi karkashin su amma Kanta yata murkushe su har suka gaji suka kyaleshi.

Don haka komai mutum ya zama a wannan daula ta Kebbi, albarkacin Muhammadu Kanta ne yake ci.

Lokacin Sarkin Muhammadu Kanta, Daular Kebbi tafi ko wace daula karfi a kasar Hausa, don har Daular Borno Kebbi taci da yaki a lokacin Kanta.

YADDA YA KAMATA A KARRAMA MUHAMMADU KANTA:

La'akari da gudumuwar Kanta na samar muna da yanci daga daular Songhai muka Zama yantattun ya'ya, Ina bada shawaran sanya wa daya ko dukkan wayannan hukumomin gwamnati dake babban birnin jaha, Birnin Kebbi sunan Muhammadu Kanta:

1- Government House-zuwa. MUHAMMADU KANTA HOUSE

2-Federal University, Birnin Kebbi, Kalgo-zuwa- KANTA UNIVERSITY, BIRNIN KEBBI

3-Sabuwar Secretariat dake Sani Abacha bye pass- zuwa- MUHAMMADU KANTA SECRETARIAT

4-Kebbi Medical Center, Kalgo-zuwa- MUHAMMADU KANTA MEDICAL CENTER

5-Presidential Lodge Birnin Kebbi-zuwa- MUHAMMADU KANTA HOUSE 

Babu wani abu da za a rasa idan aka sanyawa daya ko dukkan wayannan hukumomi sunan Muhammadu Kanta, kuma ko anyi haka ba mu biya MUHAMMADU KANTA kokarin da yayi muna ba.

Da fatar Gwamnan Jahar Kebbi Atiku Bagudu zai kafa tarihi ta hanyar aiwatar da daya daga cikin wayannan shawarwari. Idan lokaci bai bashi dama ba NA TABBATAR da magajin sa Abubakar Malami, SAN  (INSHAALLAHU) zai aiwatar da daya ko fiye daga cikin wayannan shawarwarin.
_________________

Ahmad Umar
07038182929
ahmadugamji@gmail.com

Post a Comment

0 Comments