HARIN TA'ADDANCI A SHANGA: Hon. Halima Ta Kai Ziyarar Jaje

HARIN TA'ADDANCI A SHANGA: Hon. Halima Ta Kai Ziyarar Jaje a Masarautar Yauri

Hon. Halima Hassan Tukur Yauri (Jarumar Yauri) ta jajantawa jama'ar masarautar Yauri musanman mutanen karamar hukumar Shanga da suka fuskanci harin ta'addanci wanda yayi sanadiyar hasarar rayukka da dimbin dukiya. 
Hon. Halima ta fara wannan ziyarar jaje a fadar maimartaba Sarkin Yauri, Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi, inda ta yaba da kokarin da Sarki keyi wajen inganta harkokin tsaro a Masarautar tare da addu'ar Allah Ya kawo dauwamammen zaman lafiya a Masarautar Yauri, Jahar Kebbi da ma Nijeriya baki daya. 
Hon. Halima tayi anfani da wannan damar inda ta sanar da Sarkin Yauri cewa zata tsaya takarar yar'majalisar wakilai a zaben 2027 idan Allah Ya kaimu
Daganan sai Hon. Halima ta zarce zuwa sansanin da aka kebewa yan gudun hijira a cikin garin Yauri inda ta bada nata gudumuwa tare da yin kiraga sauran masu hali da su taimaka gwargwadon hali.

Post a Comment

0 Comments