Gwamnatin Jihar Kebbi Zata Bada Muhinmanci A Fannin Tsaro

GWAMNATIN JIHAR KEBBI ZA TACI GABA DA TAIMAKAWA YAN' ASALIN JIHA DAKE SHAWAN SHIGA AIKIN SOJA___Inji SSG, Tafidan Yauri

Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu Bala Tafidan Yauri ya jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kebbi naci gaba da taimakawa matasa Yan asalin Jihar Kebbi dake bukatar shiga aikin soja da ma sauran hukumomin tsaro.
A ranar Alhamis 20/06/2024 ne aka fara tantance matasan da suka nuna shawansu na shiga aikin soja a barikin sojoji na Dukku dake Birnin Kebbi.
A duk shekara Gwamnatin Jihar Kebbi ta kan ware makudan kudade wajen tallafawa matasan da aka dauka dama sauran jami'ai da masu ruwa da tsaki a harkar daukar sojoji da sauran jami'an tsaro a Jahar Kebbi.
" Jin dadin al'umma da tsaron lafiyar su da dukiyar su sune babban kudirin Gwamnan Jihar Kebbi Dr.  Nasir Idris (Kauran Gwandu) don haka ko a wannan shekaran Gwamnatin Jihar Kebbi Zata bada taimako da ta saba bayarwa domin samun nasaran wannan aiki na daukar matasan mu a cikin rundunar sojojin Nijeriya " Inji Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu Bala Tafidan Yauri.

Post a Comment

0 Comments