YADDA JAHAR KANO TA SAITA SHIRIN AGILE



Jahar Kano Tabi Sawun Jahar Kebbi Ta Tsabtace Shirin AGILE:

Tsaftace kundin shirin AGILE na Kano; Abubuwan da aka cire da Abubuwan da aka kara a cikin kudin. 
Abubuwan da aka cire;

1. An cire dukkan hotunan da suka sabawa koyarwa addinin musulunci da al'adun mutanen Kano a cikin kundin an maye gurbin su da wadanda suka dace ( Kano dress code).

2. An cire kalmar Gender-Based Violence,  GBV (cin zarafin jinsi) an maye gurbinta da Safety & Security of children within and outside School (kare dalibai daga cutarwa a ciki da wajen makaranta), saboda kalmar GBV tana koyawa mata cewa, maza barazana ne a rayuwarsu.

3. An cire sadarar da ta baiwa mata yancin yin aikin gwamnati; "the right to work". 

4. An cire sadarar da ta baiwa yara yanchi akan iyayen su.

5. An cire sadarar da ta baiwa mata yanchin fita daga gidajen su.

Abubuwan da aka kara a cikin kundin;

1. Koyawa dalibai yanda ake alwala a aikace.

2. Koyawa dalibai yadda ake amfani da Aswaki da gawayi a wajen tsaftar baki.

3. Koyawa dalibai yadda ake tsarki a aikace.

4. Nusantar da dalibai cewa, lokacin da suke cikin jinin al'ada ba'a taba Al-Qur'ani mai girma, shiga masallaci, mu'amalar aure har sai bayan sunyi tsarki.

5. Koyawa dalibai sana'o'i da girmama iyayen su da mazajen su. E.g Made in GGSS Unguwa Uku shoes & bags.

6. Za'a fassara kundin shirin AGILE zuwa yaren larabci da ajami.

An gudanar da taron karawa juna sani na kwana biyu (13-14 Disemba,  2023) wanda aka tsaftace kundin shirin AGILE a dakin taro na Tahir Guest Palace,  Kano.

A taron akwai wakilan Sarkin Kano da Karaye; wakilan kungiyar malamai, limamai, sannan akwai HISBAH,  FOMWAN, ASSUS, ma'aikatan ma'aikatar ilimin jahar Kano, shuwagabanni shirin AGILE da yan jarida da sauran su. 

Kwamishinan ilmin jahar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa ya halarci gurin inda ya gabatar da jawabansa. Sannan ya jaddada godiyar sa ga malaman jahar Kano bisa gudummuwar su akan tarbiyar al'umma.

Allah ya taimaki gwamnatin jahar Kano. 

Abba Rabiu Gwarzo 
Member AGILE Manual review 
(13 - 14 Disemba,  2023)

Post a Comment

0 Comments